Skip to main content
SearchLoginLogin or Signup

Habashawa na iya bambanta nau'in enset da gani, amma a jinsi waɗannan 'yan uwan ​​​​ayaba suna kama da juna.

Hausa translation of DOI: 10.1101/2020.08.31.274852

Published onJul 16, 2023
Habashawa na iya bambanta nau'in enset da gani, amma a jinsi waɗannan 'yan uwan ​​​​ayaba suna kama da juna.
·

Bambance-bambancen jinsin halitta da nau'in jinsin halittu na bishiyar enset (Ensete ventricosum) da ake amfani da su a cikin magungunan gargajiya sun yi kama da bambancin da ake samu a cikin ƙasan sitaci

ShimfiƊda:

 Bishiyar enset (Ensete ventricosum) shuka ne mai amfani da yawa da ake nomawa a kudanci da kudu-maso-yammacin Habasha don abincin ɗan’adam, abincin dabbobi da faiba.

Yana ba da gudummawa ga wadatar abinci da rayuwar mutane miliyan 20.

Ana noma nau'ukan bishiyoyin enset daban-daban don amfanin su a cikin magungunan gargajiya.

Canje-canjen zamantakewa da tattalin arziƙi da asarar ilimin gargajiya na iya haifar da raguwar muhimman jinsin magunguna da bambancin jinsin su.

Duk da haka, a halin yanzu ba a sani ba ko jinsin bishiyoyin magunguna sun bambanta da sauran jinsin bishiyoyi.

Anan, mun siffata nau'ukan magunguna don tallafawa ingantaccen kiyayewa da amfani da bambancinsu.

Sakamako:

 Mun kimanta bambancin qwayoyin halittan nau’ukan bishiyoyin enset 51 wanda 38 daga cikinsu sun bayar da rahoton mafanin magani.

An gano jimlar alluna 38 a cikin 15 SSR loci.

AMOVA ta bayyana cewa kashi 97.6% na jimillar bambance-bambancen qwayoyin halitta yana tsakanin mutum da FST na 0.024 tsakanin filayen magani da marasa magani.

Wata bishiyar haɗe-haɗe ta nuna gungu daban-daban guda huɗu waɗanda ba su da alaƙa da ƙimar amfani na filaye.

Babban bincike na haɗin gwiwa ya kuma tabbatar da rashin samun gungu dabam dabam tsakanin ƙungiyoyin, yana nuna ƙarancin bambance-bambance tsakanin jinsin ƙasa da ake amfani da su a cikin magungunan gargajiya da waɗanda ke da sauran ƙimar amfani.

Kammalawa:

 Mun gano cewa nau’ukan bishiyar enset sun taru ba tare da la’akari da ƙimar amfanin su ba, ba tare da nuna wata shaida ta bambancin jinsin halitta tsakanin nau’in da aka girmar don amfanin ‘maganin’ da kuma nau’ukan da ba na magani ba.

Wannan yana nuna cewa ana iya iyakance kaddarorin magani na bishiyar enset zuwa wani adadin qwayoyin halitta, samfurin hulɗa da muhalli ko aikin gudanarwa, ko wani rahoton da ba daidai ba.

Binciken ya ba da bayanan asali waɗanda ke haɓaka ƙarin bincike a cikin amfani da ƙimar magani na waɗannan ƙayyadaddun nau’ukan bishiyoyi.


Habashawa na iya bambanta nau'in enset da gani, amma a jinsi waɗannan 'yan uwan ​​​​ayaba suna kama da juna.

Enset, wani muhimmin kayan abinci da amfanin gona na maganin gargajiya ne wanda ya kamata a kiyaye shi, yana da nau'uka iri da yawa a cewar mazauna ƙasar Habasha, amma masu bincike sun sami ɗan bambance-bambancen jinsin halittu tsakanin waɗannan nau’ukan bishiyoyi.

 “Nau’ukan bishiyoyi” ire-ire ne na shuke-shuke ko dabbobi.

A Habasha, ana amfani da nau’ukan bishiyoyi daban-daban a matsayin magungunan gargajiya don gyara karyewar ƙasusuwa, magance cututtukan hanta, ko magance zawo.

Wasu ana amfani da su don abinci, abincin dabbobi da faiba - ba a shukar bishiyar don 'ya'yanta, amma ana iya cin sassan karar.

Abin baƙin ciki shi ne, kayan aikin magani sun fi fuskantar haɗarin rasa su a zaman amfanin gona fiye da sauran nau'ukan abinci waɗanda aka fi nomawa saboda sauye-sauyen zamantakewa da tattalin arziƙin ƙasa da kuma asarar ilimin ɗan ƙasa.

 Binciken da aka yi a baya a kan bishiyar enset ya kalli shuke-shuke daga wasu wurare na musamman, amma a cikin wannan binciken, masu bincike sun binciki bambancin qwayoyin halitta na magunguna musamman, da kuma dangantakar qwayoyin da ke tsakanin nau’ukan bishiyoyi.

Ta hanyar ingantaccen fahimtar tsarin halittar bishiyar enset, masana kimiyya za su iya yin ƙarin bayanin kiyayewa don adana waɗannan tsirrai masu kima a al’adance.

 Don gano muhimman nau’ukan bishiyoyi, masu bincike sun tuntuɓi dattawan ƙauye a wurare huɗu daban-daban a Habasha.

Sun kwatanta kwayoyin halittar waxannan filayen magani da junansu da kuma samfurin filayen da ba na magani ba da ake amfani da su wajen abinci.

 Abin sha'awa shi ne, masu binciken sun gano cewa ko da yake akwai bambance-bambance a tsakanin tsirrai, babu bambancin tsarin halitta tsakanin bishiyar enset na abinci da na magani.

Har ila yau, babu wata shaida da ta nuna cewa nau’ukan bishiyoyi masu sunayen gargajiya daban-daban, waɗanda ake amfani da su don magance cututtuka iri ɗaya, na kasancewa daga nau'o'in qwayoyin halitta daban-daban.

Duk da haka, masu binciken sun lura da kusancin jinsin halittu tsakanin tsirrai da aka gano da wani suna na yare, wanda ke nufin mutanen yankin suna da kyakkyawar iya ganewa da gani, da bambance tsakani, da takamaiman nau’ukan bishiyoyi.

 Waɗannan binciken suna ƙara haɓakar ilimin halittar ɗan’adam, wanda ke taimakawa ƙoƙarin kiyayewa don bambance tsakanin ciyayi masu mahimmancin magani.

Wannan bayanan qwayoyin halitta na iya taimakawa wasu masu bincike su bincika kaddarorin magani na bishiyar enset nan gaba.

 Masu binciken sun nuna dalilai da yawa kan kamannin qwayoyin halittar da suka samu.

Alal misali, yana yiwuwa duk tsirrai na nau’in bishiyar enset suna da amfani wajen magani, amma an fi son wasu nau'o'in tsirran bisa ga dalilai na al'ada.

Hakanan yana yiwuwa cewa ƙimar magani na wasu tsirrai yana da alaƙa da yanayin wajen da suke, tare da cewar tsirrai na samun abubuwan magani na musamman a ƙarƙashin wasu yanaye-yanaye da suka girma a ciki.

Nan gaba, kwatancen sinadarai na nau'ukan bishiyoyi daban-daban na iya buɗe zurfafan fahimtar ƙimar maganinsu.

Wannan binciken ya kasance wani ɓangare na babban haɗin gwiwa tsakanin masu bincike na Burtaniya da Afirka da nufin inganta amincin abinci da fahimtar yuwuwar magunguna na shuka.

Connections
1 of 5
Comments
0
comment
No comments here
Why not start the discussion?