Skip to main content
SearchLoginLogin or Signup

Yawaitar ciwon jijiyar qwaqwalwa da qashin baya mai alaqa da ciwon suga

Hause translation of DOI: 10.1186/s12902-020-0534-5

Published onMar 30, 2023
Yawaitar ciwon jijiyar qwaqwalwa da qashin baya mai alaqa da ciwon suga
·

Yawaitar ciwon jijiyar qwaqwalwa da qashin baya mai alaqa da ciwon suga a Afirka: Tsarerren Waiwayen Aiyuka da suka Gabata

ShimfiƊda

Ciwon suga matsala ce ga kiwon lafiya a duniya wanda zai iya kawo babban matsalar tattalin arziki.

Yawaitar ciwon jijiyar qwaqwalwa da qashin baya mai alaqa da ciwon suga sanannen matsalar ciwon suga ne wanda ke qara awkuwar kurquncewa.

Ko da yake akwai bammanci da yawa cikin binciken da aka yi kan yawaitar ciwon jijiya cikin masu ciwon suga a Afirka.

Saboda haka wannan binciken nna nufin gano yawaitar ciwon jijiya cikin masu ciwon suga a Afirka.

Hanyoyi

An binciko PubMed, Scopus, Google Scholar, African Journals OnLine, kundin Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya kan Afirka da Cochrane Review daga intanet don tsamo muqalu masu alaqa da batun.

A bin tsarin Preferred Reporting Items for Systematic Review and Meta-Analysis (PRISMA).

An gwada bambanci tsakanin binciken ta hanyar tsarin rashin daidaito wato (I2).

An yi amfani da tsarin funel plot da tsarin baibai na Egger don gano son rai ke cikin ko wani bincike.

An yi amfani da tsarin gano tasiri don gano yawaitar ciwon jijiyar qwaqwalwa da qashin baya mai alaqa da ciwon suga cikin marasa lafiya a Afirka.

An yi amfani da tsarin kwatanta bayanai ta hanyar na’urar STATA™ kashi na14.

Sakamako

Binciken ya haxa da aiyuka ishirin da uku wanda ya haxa da mutane 269,691 cikin nazarin.

A taqaice dai, an samu yawaitar ciwon jijiyar qwaqwalwa da qashin baya mai alaqa da ciwon suga a 46% (95% CI:36.21–55.78%).

Bisa lura da yankunan Afirka dabamdaban, an gano cewar an fi samun yawaitar ciwon jijiyar qwaqwalwa da qashin baya mai alaqa da ciwon suga a Afirka ta yamma da kasha 49.4% (95% CI: 32.74, 66.06).

Kammalawa

Wannan binciken ya nuna cewa gaba xayan yawaitar ciwon jijiyar qwaqwalwa da qashin baya mai alaqa da ciwon suga ya da yawan sosai a Afirka.

Saboda haka, yawaitar ciwon jijiyar qwaqwalwa da qashin baya mai alaqa da ciwon suga na buqatar matakai daidai da yanayi da matakan kariya na musamman a ko wani qasa.

Akwai buqatar qarin nazarin bayanai don gano abubawan masu alaqa da aukuwar yawaitar ciwon jijiyar qwaqwalwa a qashin baya mai alaqa da ciwon suga.


Yawaitar ciwon jijiyar qwaqwalwa da qashin baya mai alaqa da ciwon suga

Akwai yawaitar gurvacewan jijiya cikin masu ciwon suga a Afirka, fiye da ko wani yanki a duniya.

Masu bincike sun ce dole ne Afirka ta qara saka jari da kayan aiki da maida hankali kan wannan ciwo mai tsanani.

Ciwon jijiyar qwaqwalwa da qashin baya mai alaqa da ciwon suga shi ne sakewa, daskarewa, da ciwo wanda lalacewar jijiya ke haddasawa saboda ciwon suga, wanda shi ne cutar da ke sa jikin xan’adam ya kasa daidaita mizanin sugar jini yanda ya kamata.

Bincike da dama sun yi aiki kan yawaitar ciwon jijiyar qwaqwalwa da qashin baya mai alaqa da ciwon suga, sai dai sakamakon binciken ya bambanta sosai, inda aka samu misalai kamar 8.4% a China, 48.1% a Sri Lanka, da 29.2% a India.

Haka ma ake samun bambancin sakamako a Afirka, misali an samu 71.1% a Najeriya, 16.6% a Ghana, da 29.5% a Habasha.

A wannan binciken, masu bincike sun yi nazarin rahotanni daga Afirka don samun sahihiyar fahimta a kan yawaitar cutar.

Masu binciken sun binciko kundayen ajiya na intanet na PubMed, Scopus, Google Scholar, African Journals OnLine, kundin Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya kan Afirka da Cochrane Review don samo muqalu kan batun.

Binciken ya yi amfani da tsarin waiwaye da aka fi sani da Preferred Reporting Items for Systematic Review and Meta-Analysis (PRISMA) don kwatanta dukkan binciken da aka yi ta hanyar tsarin lissafi mai yawa.

Sun zavi aiyuka 23 da aka yi kan jumillar mutane 269 691.

Masu binciken sun yi amfani da aiyuka 10 daga Najeriya, 4 daga Habasha, 2 daga Kamaru, 2 daga Sudan, 2 daga Masar, da 1 kowanne daga Ghana, Uganda, da Tanzaniya.

A taqaice dai, sun gano cewar yawaitar ciwon jijiyar qwaqwalwa da qashin baya mai alaqa da ciwon suga cikin masu ciwon suga ya kai 46% a faxin nahiyar Afirka, kuma ya fi yawa a jammacin Afirka wanda ke da 49.4%.

Wannan sakamakon ya yi kama da sakamakon da aka samu qan kasahe masu tasowa kamar Iran wanda aka samu 53%.

Savanin haka, nazarin da aka gudanar kan qasashen da suka ci gaba ya nuna yawaitar ta tsaya a 35.78% kacal, wanda ke nuni da cewar ya kamata qasashe masu tasowa su taimakawa masu ciwon suga wajen kula da sugar jininsu don kare kuvacewar jijiya

Masu binciken sun yar cewa sun dubi muqalu da aka wallafa da harshen ingilishi ne kawai, saboda haka sun bar marasa lafiya na wasu harsuna kamar Sipaniyanci, Faransanci da Potugis.

Wani givin binciken kuma shi ne masu binciken yi amfani da bayanai da aka samu daga asibiti ne kawai, wanda hakan ya bar da yawa daga cikin mutane masu ciwon suga a baya.

Wannan binciken ya nuna cewa masu ciwon suga da daman a Afirka na fama da qurvacewar jijiya da ke alaqa da ciwo.

Kan wannan sakamakon ne masu binciken ke ba da shawar qasashen Afirka su aiwatar da matakai da suka dace da kevavvun yanayi da matakan kariya don taimakawa masu ciwon suga.

Connections
1 of 5
Comments
0
comment
No comments here
Why not start the discussion?